Da Dumi Dumi: An yankewa dan Abdurrashid Maina Faisal hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari saboda laifin halatta kudin haram.

An yanke wa Faisal Maina, dan tsohon Shugaban Kwamitin Kwaskwarimar Fansho, Abdulrasheed Maina hukuncin daurin shekaru 14.

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yanke wa Faisal hukunci a yau Alhamis.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Okon Abang ya samu Faisal da laifi kan laifuka uku na halatta kudin haram.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ce ta gabatar da Faisal a gaban kotun.

Ana

tuhumar Faisal tare da mahaifinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *