Da dumi dumi: Dan ta’adda Bello turji ya saki mutun 52 da yayi garkuwa dasu a Jihar zamfara.

Shahararran Dan bindiga da ya yi kaurin suna a jihar Zamfara, Bello Turji, a ranar Litinin ya sako mutane 52 da aka dade dayin garkuwa da su, kamar yadda majiya mai tushe ta shaida wa Daily Trust.

“A halin yanzu ana kwashe wadanda aka sako daga dajin zuwa wani wuri da aka amince da su inda za a kai su garin Shinkafi.

An jera motocin bas kuma an umurce su da su fara tafiya zuwa Maberiya, wani yanki mai tazarar kilomita 5 daga gabashin garin Shinkafi,” wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu.

Turji

shi ne jagoran kisa da garkuwa da mutane a yankunan kananan hukumomin Shinkafi – Sabon Birni da Isah na jihohin Zamfara da Sokoto.

A watan da ya gabata, Turji ya rubuta wasikar majalisar masarautun Shinkafi, yana mai jaddada aniyarsa ta ajiye makamansa tare da rungumar zaman lafiya.

Majiyoyi sun ce wani bangare ne na tattaunawa da Turji wanda ya kai ga sako wadanda aka yi garkuwa da su.

Cikakkun bayanai zai Zo daga baya…

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *