‘Da Dumi Dumi: Gwamnatin Jihar kaduna ta Hana hawa babura da adaidaita sahu.

A wata sanarwa da Gwamnatin Jihar ta fitar a Yau tana Mai Cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta Dauki Matakan Dakile Ayyukan Ta’addanci Muna amfani da wannan kafa ta Facebook domin sanar da al’umma matakan da muka ɗauka a ƙoƙarin da muke yi na daƙile ayyukan ta’addanci kamar yadda jami’an tsaro suka ba mu shawara. Waɗannan matakai sun haɗa da:

  1. Rufe layukan sadarwa a wasu yankunan jihar
  2. Hana amfani da babura (mashin) a duk fadin jihar har na tsawon wata uku.
  3. Hana mallakar makamai
  4. Hana amfani da Keke Napep bayan karfe bakwai na yamma zuwa karfe shida na safe, sannan kuma an hana su amfani da labule.
  5. Hana sayar da man fetur a jarakuna a Karamar Hukumar Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kachia da Kagarko da Kajuru.
  6. Hana safarar gawayi da itace
  7. Hana safarar dabobbi; shigowa da fita da su wajen jihar
  8. Hana cin kasuwannin sati-sati ko mako-mako a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kasuwar Kawo da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa

Muna bayar da haƙuri na halin ƙunci da al’umma za su shiga saboda waɗannan matakan. Duk waɗannan matakan da muke ɗauka muna ɗauka ne saboda kare rayuka da dukiyoyin al’ummarmu.

Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifar, ya tona asirin waɗannan ‘yan ta’addan da masu ɗaukar nauyinsu. Amin

One thought on “‘Da Dumi Dumi: Gwamnatin Jihar kaduna ta Hana hawa babura da adaidaita sahu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *