Da ‘dumi ‘dumi Jirgin ruwa ya kife da mutun Arba’in a ruwan bagwai dake Jihar Kano mutun goma sun mutu.

Rahotanni daga Jihar Kano na Cewa wani jirgin ruwa wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai ta jihar Kano ya samu hatsari a cikin ruwan inda ya kife da mutane 40 harda matukin Jirgin, a halin Yanzu an ceto rayukan mutun hudu inda aka ciro gawar mutane 10 sannan ana cigaba da Kokarin ceto ragowar mutanan.

Wannan shine karo na biyu da wannan hadari ya taba faru a wanan Karamar Hukuma ta Bagwai dake jahar Kano inda ko a wancan Lokacin ma anyi a sarar rayuka da dama, muna rokon Allah Ya kawowa Al’ummar wannan yanki mafuta.

Daga

Comr Aliyu Abdul Garo
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *