Da Dumi Dumi: Kamfanin Twitter ya rubutowa Najeriya wasiƙar neman yafiya, inda yace ya tuba.

Tambarin Tuwita

Gwamnatin tarayya ta sanar da buƙatar da kamfanin tuwita yayi gareta ta hanyar rubuta wasiƙa mai cike da nadama da roƙon iri akan a zauna teburi guda domin warware duk wani saɓani da aka samu tsakanin ɓangarorin guda biyu.

Idan za’a iya tunawa, Gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakatar da kamfanin na twitter ne daga ƙasar nan sakamakon goge maganar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kamfanin yayi, nuna goyon baya ga fafutukar Endsars da kuma kafa Ofishin kamfanin na Afirka da sukayi a Ghana, wanda hakan baiyiwa gwamnatin Najeriya daɗi ba.

Tambarin Tuwita

Ministan yaɗa labarai na ƙasa Lai Muhammad ne ya bayyana haka yayin gudanar da wani shiri a wani gidan radiyo da safiyar yau talata.

A cewar sa:

“Ina mai tabbatar muku da cewa, kamfanin Tuwita ya rubuto mana wasiƙa yana neman a sasanta, since sunyi nadama sosai”

“Kuma mu daman tunda fari, munce kofar mu a buɗe take domin sasantawa da masu neman sulhu”.

Sai dai kuma ministan, ya ƙara nanata matsayar gwamnati na cewa, bazata lamunci ko wani irin kamfani mai neman tada zaune tsaye ba, kama daga kamfanin cikin gida ko kuma kamfanin dake zaune a waje.

Lai Muhammad yace, gwamnatin tarayya ta gindaya wa kamfanin na tuwita wasu sharuɗɗa, wanda dole sai ya yarda dasu sannan za’a basu damar gudanar da harkokin su a Najeriya.

Cikin ka’idojin sun haɗa da yin rijista da gwamnati, da sahalewar gwamnati akan yanayin labaran da za’a dinga wallafawa a shafin duba da irin tasirin da yake dashi ga al’ummar ƙasar.

Tuwita

Shin kamfanin na tuwita zai amince da waɗannan sharuɗɗa? Lokaci ne kawai zai nuna mana.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

One thought on “Da Dumi Dumi: Kamfanin Twitter ya rubutowa Najeriya wasiƙar neman yafiya, inda yace ya tuba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *