Da Dumi Dumi majalisar dattijan ta aminta Buhari ya karbo bashin tiriliyan N2.3.

Majalisar dattijai yau ranar Laraba, ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari na ciyo bashin tiriliyan N2.3 (kwatankwacin dala biliyan 6.183) don biyan gibin a cikin Dokar Kasafin Kudin ta 2021.

Wannan ya biyo bayan la’akari da rahoton kwamitin ne na basusukan cikin gida da na waje, karkashin jagorancin Sanata Clifford Ordia (PDP, Edo).

A watan Mayu ne Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa don samo bashin daga hanyoyin da dama, ciki har da masu ba da rance daga bangarori da dama, da kuma Kasuwa Duniya (ICM) ta hanyar fitar da Eurobonds.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *