Da Dumi Dumi ‘yan Bindiga sun kashe mutun 13 sun Kuma Kone ofishin’yan Sanda a jihar Niger.

‘Yan bindiga sun kai hari garin Beri da ke gundumar Bobi a jihar Neja, inda suka kona wani ofishin‘ yan sanda tare da kashe mutane sama da 13, ciki har da wani jami’in dan sanda.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Neja ce ta ruwaito harin a cikin wani rubutu a ranar Litinin kuma ya zo ne kwana daya kacal bayan sace dalibai 200 daga wata makaranta a jihar.

A cewar hukumar agajin gaggawa, harin ya yi sanadiyyar jikkata mutane da dama.

‘Yan

fashin sun kuma kai hari Unguwan Malam Bako a gundumar Kotonkoro inda suka yi awon gaba da wasu mutane da ba a tabbatar da adadin su ba, in ji hukumar.

Hukumar ta zayyana sunayen mamatan kamar haka: Idris Ahmed Kwata, Hadiza Umaru Tunga, Momi Dalladi, Ibrahim Dalkadi, Yau Dalladi, Saadiya Garba, Garba Umar Tashanjirgi, Hussaini Shuaib, Ayuba Garba, Abdullahi Jodi, Alhaji Isah Kasakohi da Fatima Nasiru Kwata .

Jihar Neja, na daya daga cikin jihohin da ‘yan fashi ke addabar su a fadin kasar.

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello ya bayyana yanayin rashin tsaro a matsayin “yanayin tsanani

“Yanayin ya kai matakin rikici, a zahiri yanayi ne na yaki da ya kamata mu fuskanta ba tare da wani bata lokaci ba,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *