‘Da ‘dumi ‘dumi ‘yan Bindiga sun sace mutun talatin da shida 36 a jihar kaduna.

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai farmaki Jangali Bagoma da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna tare da yin garkuwa da mutane 36. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi da jiya.

Malam Abubakar Mohammed, wanda mazaunin Birnin Gwari ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna.

Ya ce, “’yan bindigar sun kai farmaki kan al’umma a jiya da safe (Litinin) inda suka yi garkuwa da mutanen kauyen, ciki har da mata da kananan yara.

“Ba

su kashe kowa ba yayin hare-haren. Har yanzu muna tattara alkaluman mutanen da suka yi garkuwa da su a yau (Litinin)”.

Ya koka da yadda ‘yan bindigar suka kai wa al’ummar garin hari sau biyu cikin sa’o’i 24, lamarin da ya bayyana a matsayin mai ratsa zuciya.

Idan za a iya tunawa, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mazauna Ungwa Gimbiya 50 a karamar hukumar Chikun a safiyar ranar Juma’a, 3 ga Disamba, 2021.

Mohammed ya ce “Yan Najeriya ba su da tsaro a gidajensu, wadannan mutane suna sace mutanenmu ko ta yaya, ko da yaushe.
Ya kamata gwamnatinmu ta yi wani abu ta kawo karshen wannan garkuwa da mutane, ba za mu iya ci gaba a haka ba,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi domin tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya, ya kara da cewa.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Mohammed Jalige, ya yi alkawarin Sanar damu bayan ya tabbatar da faruwar lamarin wanda har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto a jiya Bai Kira ba.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *