Da ‘dumi ‘dumi ‘yan Bindiga sun shiga har cikin Jami’ar Abuja sun sace ma’aikata

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wasu ma’aikatan jami’ar Abuja.

A cewar majiyoyin, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata.

Wani mazaunin garin Dzarma Idris ya shaida wa majiyarmu cewa da misalin karfe 12:14 na safe ne aka fara harbe-harbe a kaikaice kafin daga bisani wasu ma’aikatan suka tafi da su.

Wani mazaunin garin ya ce an sace mutane bakwai a harin.

Ya ce ‘yan bindigar sun shafe sama da sa’o’i biyu suna aikin.

Da take tabbatar da harin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta ce jami’an tsaro na kan gaba a lamarin.

Ba

ta bada cikakken bayani na adadin mutanen da aka sace ba.

Jami’ar ta kuma tabbatar da faruwar lamarin amma ba ta bayar da cikakken bayani kan ma’aikatan da aka sace ba.

“Wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari an ma’aikatan Jami’ar da sanyin safiyar yau.”

“Jami’an tsaron mu, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, sun hada kai domin tabbatar da tsaro a kwaryar Makarantar

“Mun samu rahoton cewa ma’aikatanmu hudu da ‘ya’yansu, duk da haka, miyagun mutanen sun yi garkuwa da su. Ana kokarin ganin sun dawo lafiya. Ranar bakin ciki ne a gare mu, hakika, “in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *