Da d’uminsa: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

Kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biafra ta soke dokar tilastawa mutane zaman gida da ta saka a kudu maso gabas.

IPOB ta soke dokar ne ana kwana biyu kafin yin zaben gwamnan jihar Anambra wadda a baya ta ce ba za a yi ba sai an sako Nnamdi Kanu.

A wani abu mai kama da mi’ara koma baya, IPOB ta soke dokar ta bukaci mutanen Anambra su fita su yi zabe ta tare da fargaba ba.

Daga

Ahmad Aminu kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *