Da duminsa: An kashe Auwalun Daudawa.

Idan ajali yazo hakika dole atafi. Kwanakin baya kaɗan da suka wuce an ruwaito cewa Auwalu Daudawa dan bindigar nan da ya jagoranci garkuwa da daliban sakandaren Kankara da ke jihar Katsinan Najeriya, ya kuma tuba sannan ya sake komawa ruwa a wannan makon.

Kwamishinan Tsaro da Lamurran Cikin Gida na jihar Zamfara Abubakar Justice Dauran ya tabbatarwa da majiyarmu cewa, tabbas a wannan yammaci, Auwalu ya sheƙa barzahu.

class="has-text-align-justify">Kwamishinan ya ce Auwalun Daudawa ya shaida masu cewa ya tafi bikin ‘yan uwansa amma abun takaici ashe daji ya koma kuma da bai wata wata ba ya koma ruwa, inda ya kore garken dabbobin wasu Fulani inda nan take suka bindige shi.

To Allah ya kyauta.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

One thought on “Da duminsa: An kashe Auwalun Daudawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *