Dalilin dayasa Sanata Uba sani ya sami nasara Yazo na ‘daya a majalisar dattijan Nageriya ~Bello El’rufa’i.

A Cikin wani sako daya fitar Dayake tofa albarkacin bakinsa Shugaban ma’aikata na gidan Sanata uba sani Bello El’rufa’i Yana Cewa Dangane da rahoton Midterm na Majalisar Dokokin ta kasa ya zuwa Yanzu Sanata Uba Sani ya kasance a matsayin sanata mafi kololuwa ta fuskar yawan aiki a majalisar dattijai ta 9

Wannan nasara da ci gaban ba zai rasa nasaba da kasancewar daukar nauyin kudrin dokar da Sanatan yayi har ashirin da daya 21. Wanda daya 1 daga cikin guda 21 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sakawa hannu a matsayin doka, biyar 5 sun wuce sharudan majalisar dattijai, hudu 4 na kan jiran tattaunawar Majalisar, Wanda Kuma Sha hudu 14 anyi musu karantawa a karon farko.

Manyan Kudirorin na doka sun Kasance kamar Haka.

1 Banks and Other Financial Institutions (Repeal and Re-Enactment) Act 2020 (SB.178) Wanda
Mai Girma, Shugaba Muhammadu Buhari GCFR ya tabbatar da shi yanzu haka ya zama doka a Tarayyar Najeriya Wanda ya gabata a ranar 13 ga Nuwamba 2020.

  1. Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Giwa Jihar Kaduna (Est, Etc) Bill 2019 (SB. 121). Wannan doka tana jiran amincewar Wakilan Majalisar.
  2. Federal Medical Center Rigassa, Jihar Kaduna (Est., Etc.) Bill 2019 (SB.169). Wannan kudrin doka yana jiran amincewar Wakilan Majalisar.
  3. Dokar Makamai Cap F28 LFN (Gyarawa) Bill 2020 (SB. 549). Wannan Kudrin Dokar itama tana jiran amincewar Wakilan Majalisar.
  4. Dokar Gudanar da Dukiya ta Najeriya (Kwaskwarimar) Bill 2021 (SB. 669). Har’ila yau Wannan doka tana kan teburin mataki na Kwamiti a Majalisar ~Inji Bello El-Rufai wanda shine
    Shugaban Ma’aikata SLA na Sanata Uba sani

Sanata uba sani shine Sanata mafi Samun yabo a majalisar dattijan duba da irin aikace aikacen alkhari da yake gudanarwa musamman wajen koyar da matasa sana’o’i tare da Samar da jari a gare su duk domin dogaro da Kai a yankinsa na kaduna ta tsakiya da Jihar kaduna Kai dama kasa Nageriya Baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *