Dan uwan ​​Dangote, Sani, ya rasu a asibiti a Amurka

Mataimakin shugaban rukunin Dangote kuma mai kamfanin Dansa Agro-allied Limited, Sani Dangote ya rasu.

Ya kasance kanin attajirin Afrika, Aliko Dangote.

Majiyoyin dangi guda biyu sun tabbatar wa Jaridar DAILY NIGERIAN rasuwar, inda suka ce Mista Dangote ya rasu ne a wani asibitin Amurka da yammacin Lahadi bayan ya sha fama da jinya.

Mista Dangote hamshakin dan kasuwa ne wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana gogewa a harkar kere-kere, noma da kuma ayyukan mai.

Ya

zauna a kwamitin wasu kamfanoni da dama kuma shi ne mataimakin shugaban kungiyar masu sana’ar Gum, dan cibiyar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya kuma shugaban kungiyar masu sana’ar takin zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *