Datti Assalafy Ka fara bayyana sunan ka da Addreshin ka kafin kayi wa Sheikh Nuru Khalid rashin kunya ~Cewar sani Zangina

Batun Sheikh Nuru Khalid A Lokacin da yake maida martani ga Datti Assalafy sani Ahmad zangina Yana cewa Duk Addini ko Akidar da Dan Adam yakeso yabi ko yakebi tohfa lallai yana bukatar rayuwa kafin ya iya bin wannan addinin ko akidar.
Dama dai nasan cikakken sunanka ne dana maka martanin daya dace dakai, toh amma bakada sunan yanka bare na uba ballantana na kiraka da sunan.
Toh amma tunda ka sauya wanda kake ganin kafi aminta dashi toh sai muce Allah raka daki gona.

In

kanada karfin halinda zakawa Malami irin Sheikh Nuru Muhammad Khalid rashin kunya, toh kana bukatar zarra dazaka iya bayyana kanka da cikakken suna da adireshenka.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid cikakken ahlus Sunnah ne wanda baya bukatar amincewarka ko iyayen gidanka.

Duk kashe – kashenda akeyi a kasarnan musamman a arewacin Najeriya Malamanmu sunyi shiru wadanda kai da ire irenka da kuke da awar sune ahlus Sunnah na gaskiya.

Sheikh Albanin Gwambe an dakatar dashi dan ya fadi gaskiya, Abu Ammar a katsina har kakkamashi anyi saboda ya fitar da gaskiyar da su Malam Bala Lau dasu Kabir Gwambe basu fada ba. An kamo Sheikh Bello yabo tundaga sokoto har kaduna dan yafadi gaskiya.

Inda kawai kukafi apki shi ne inda za adora gwamna kan mumbari a yaudareshi yayi wa azi ya bada kudi, tunda kudai in zaku samu kudi toh rayuwar bayin Allah ba a bakin komi take ba.

Abinda kukafi aminta dashi shi ne me yasa ake maulidi, kuma me yasa baza abari ba? Kokai aka tambaya cewa yaushe za abar maulidi bansaran zaka bada wannan amsar ba.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid cewa yayi abar zagin mai maulidi ko sukarshi shima mai maulidi ya dena aibata wanda baya maulidi har muje gaban mai abun yayiwa kowa hisabi.

Saboda haka ina mai jamaka kunne da lallai ka kula da harshenka kan wadannan kalaman dakake sukar Malaminmu dasu.
Sako daga
Sani Zangina Daura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *