Dogo Giɗe, hatsabibin shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara

Dogo Gide, hatsabibin dan bindiga, ya saka dokar hana siye da siyar da giya da sauran muggan kwayoyi a wasu garuruwan masarautan Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Shugaban ‘yan bindigan da ke zaune a dajin Kuyambana, da ya ratsa ta jihohin Zamfara, Kaduna, Niger da Kebbi ya kwace iko a garin Babbar Doka.

A satin da ya gabata, yaran sa sun kashe wani shugaban yan bindigan da ake kira Damina.

Ya

gargadi mazauna kauyukan cewa a bainar jama’a za a kashe duk wanda aka kama yana sayar da miyagun kwayoyi ko kuma shan su.

Wata majiya ta shaida cewa tunda farko Gide ya kwace miyagun kwayoyi daga wasu da ake zargin dillalai ne sannan ya cinna musu wuta. Ya kuma kidaya kudin kwayoyin ya biya wadanda suka yi safarar su, ya gargadi yaransa da sauran yan kauyen su dena shan miyagun kwayoyin.

Majiyar ta kara da cewa: “An kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi ciki har da wani Zakin Goro a yayin da aka kai sumame gidan masu kwarmatawa yan bindiga bayanai.

“Wasu lokutan, bata garin na zuwa shagunan sayar da magani su siya miyagun kwayoyin.

Su kan yi wa kansu allurar Pantazocine su tafi bayan shan wasu kwayoyi irin su Tramadol da sauransu.

“Amma yan bindiga suna yawan siyan wani allura mai suna Pentazocine kuma ana dillalan miyagun kwayoyin da suka zama masu kai wa yan bindiga bayanai ke kai musu cikin daji.”

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *