EFCC ta kwato naira Bilyan 152bn daga barayin nageriya.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta bayyana a ranar Litinin cewa a shekarar 2021 ta kwato kimanin bilyan N152,088,698,751.64; $386,220,202.84; £1,182,519.75; €156,246.76; 1,723,310.00 Saudi Riyal, 1,900.00 Rand na Afirka ta Kudu, da dalar Kanada 1,400.00 tsakanin watan Janairu zuwa Disamba.

A cewar mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, farfadowar ta kuma hada da na’urar kudin dijital da 5, 36957319 Bitcoin da 0.09012 Ethereum.

Hedikwatar Hukumar ta mamaye kudaden da aka kwato da N67,249,744,994.89, $375,662,223.59 da £1,151,539.75. reahen Hukumar ta Legas ce ke biye da ita, wacce ta jagoranci kwato Naira da N70, 315,611,260.52, $9,286,497.83 da £21,500.00.

Rundunar

shiyar Kaduna ta zo na uku a fannin kwato Naira da jimillar Naira 3, 339,405,723.93 yayin da Rundunar shiyar Ibadan ta dauki matsayi daya wajen kwato Dala amurka har dala $387,385.00.

Da yake karin haske game da ayyukan, Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa kudaden an kwato su be kai tsaye visa tsarin matakan gwamnati daban-daban (Majalisun a Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi), kungiyoyi da kuma daidaikun mutane (wadanda aka aikata laifuka) a cikin shekarar data gabata.

Ya yabawa ma’aikatan hukumar bisa wannan aiki tare da Kiran su da su kara himma wajen ganin an hana masu aikata laifukan tattalin arziki da kudi cin gajiyar abin da suka samu a fannin aikata laifuka.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *