El Rufa’i ya tsige Shugaban ma’aikatansa Jim ka’dan bayan ya kira Sanusi Lamido da kalmar Tsohon sarkin Kano.

Rahotanni dake yawo a kafafen sada zumuntar Zamani na Cewa Gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar kaduna ya sauke Muhammad Sani Dattijo Shugaban Ma’aikatan (COS) fadar gwamnatin sa Jim ka’dan bayan ya Kira Muhammadu Sanusi Lamido Na II da sunan “tsohon Sarkin Kano”

A Cikin wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumuntar Zamani daga jiya Zuwa yanzu, an hasko Dattijo Shugaban ma’aikatan Yana Kiran khalipan na Tijjaniya da sunan Tsohon sarkin Kano Lamarin da yasa Muhammadu Sanusi Lamido Na II, yin gargadi ga Shugaban ma’aikatan dattijo Yana Mai Cewa a nan Gaba idan zaka kirani karka sake kirana da sunan Tsohon sarkin Kano.

class="wp-block-video">https://www.jaridarmikiya.com/wp-content/uploads/2021/10/Video-53.mp4

Biyo Bayan Haka jim ka’dan Malam Nasir Ahmad El’rufa’i ya sauke Shugaban ma’aikatan ba kuma ba tare da bayyana dalili ba, amma a Lokacin da Mikiya ta tuntuɓi wani na kusa da Gwamnan wanda bashi bukatar mu bayyana sunansa yace damu ko ka’dan Babu kamshin Gaskiya game da Batun Cewa an sauke Shugaban ma’aikatan ne Sakamakon ya Kira khalipan da sunan Tsohon sarkin Kano kawai an sauke shi ne domin gwamnatin na da shirin sauye-sauye kamar yadda ta fitar da Jerin wasu ma’aikatan ta da aka chanja masu wajen aiki.

Kawo yanzu dai El’rufa’i ya nada Shugaban ma’aikatan Muhammad Sani dattijo amatsayin Kwamishinan kasafin ku’di da Tsare Tsare kamar yadda gwamnatin jihar ta bayarda da sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *