El’rufa’i Yace Zai sadaukar da diyyar Milyan goman 10m ga Gidan nakasassu idan Gidan jaridar Suka biyashi hakki sa da kotu ta umarta.

A wata sanarwa da Muyiwa Adekeye
Mashawarci na Musamman Kan Sadarwa ga Malam Nasir El-Rufai ya yi na’am da hukuncin da babbar kotu ta yanke a kan karar da ya shigar a kan mawallafin jaridar The Union. A watan Yulin 2015, kasa da watanni biyu da zamansa gwamnan jihar Kaduna, idan ba a manta kungiyar kwadago ce ta buga labarin karya kan bayyana kadarorinsa. Dan jaridan da ya gabatar da labarin ya dogara ne akan kalaman nasu na bangaranci da jita-jita da kuma tunanin tserewa hukunci Kamar yadda gwamnatin jihar kaduna ta bayyana.

Gwamnan

ya yi gaggawar fitar da sanarwar karyata labarin a ranar da aka buga shi kuma ya tabbatar da aniyarsa ta zuwa kotu domin ta bi Masa hakkinsa. Justice M.L. Mohammed ya yanke hukunci a shari’ar a jiya, 1 ga Nuwamba, 2021, shekaru shida bayan shigar da karar.

Dayake fitar da sanarwar Malam El-Rufai ya yi maraba da hukuncin da kotun ta yanke a ya Kuma ce ’yanci da samun lasisin Aikin jarida ba Yana nufin bata sunan mutane bane ko sanya jita-jita a matsayin aikin jarida. Bayan diyya da aka bayar da kuma uzurin da kotu ta bayar, wannan hukuncin ya sake tabbatar da fiffiko na gaskiya da tabbatar da dacewa a aikin jarida. Malam El-Rufai yayi Alkawarin zai bayar da diyyar N10m da kotu zata bayar ga asusun kula da nakasassu na jihar Kaduna.

Ta hanyar zuwa kotu da kuma bayar da shaida a kan lamarin Malam El-Rufai ya nuna imaninsa kan bin doka da oda, matakin da ya dauka a shari’o’in da ya gabata, inda ya nemi gafara da kuma janyewa daga wasu jaridun. Wannan ya sanar da ci gaba da bin wasu shari’o’in na bata suna a kotuna.

Gwamnan ya godewa tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin A.U. Mustapha (SAN), saboda jajircewar da suka yi wajen ganin lamarin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *