Gamayyar kungiyoyi ashirin da hu’du 24 sun karrama Sanata Uba Sani da Lambar yabo amatsayin Sanata mafi aiki a duk Majalisar dattawan Nageriya.

Gamayyar kungiyoyi ashirin da hu’du 24 a yankin Arewa sun zabi Sanata Uba Sani a matsayin wanda zai karbi kyautar jagoranci na kwarai, bisa la’akari da irin yadda yake gudanar da al’amuransa na shugabanci a majalisar dattijan Nageriya.

Gamayyar kungiyoyin da Alhaji Bello Abdulhamid amatsayin mai gabatarwa da Muhammad Kabir, sakataren yada labarai, Ibrahim Tanimu, ya wakilta, sun shaida wa manema labarai a Kaduna cewa yanzu lokaci ya yi da za a karrama ire-iren hazikan ‘yan majalisa irin su Sanata Uba Sani wanda ya yi fice a harkokinsa na majalisa ya Kasance Mai tasiri mai kyau a kan rayuwar Jama’ar da yake wakilta.

Bayan

tantancewar da muka yi, mun kammala tare da gano cewa Sanata Uba Sani, Shugaban Kwamitin Bankuna, Inshora da sauran cibiyoyin kudi na Majalisar Dattawa, ya cancanci babbar lambar yabo ta Shugabanci na kwarai.”

“Kungiyoyin da suka bayarda wannan lambar yabo sun haɗa da Kungiyar Unified Awareness Forum (UAF), Northern Youths Grand Alliance (NYGA), Women Empowerment Network (WEN), Grassroots Mobilisation Organisation (GMO), da kuma sauran 20.

“Wannan karramawa ta kasance a cikin girmamawa da kuma godiya ga gaskiyar cewa shi dan Najeriya ne na kwarai” in ji su.

Gamayyar kungiyar ta bayyana cewa fitaccen dan majalisa Sanata Uba Sani Wanda yayi tsaye a fagen fafutukar kare hakkin bil’adama, da irin nasarorin da ya samu a matsayinsa na Mai ba da shawara S.A ga Tsohon Shugaban kasa Obasanjo da Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i, kuma a matsayinsa na fitaccen Sanatan Tarayyar Najeriya, na daga cikin abubuwa da Suka nuna ya cancanci a ba shi wannan lambar yabo.

Musamman a Ayyukan sa na shigar da tsarin gyaran dokokin wanda ba a taba ganin irin haka ba, tawali’u, tausayi ga talaka, jajircewarsa da kokarinsa ta hanyar samar da mafi kyawun shugabanci ga kwamitin Majalisar Dattawa kan Bankin, Inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi, wanda ya bunkasa Tattalin Arzikin Nijeriya a dunkule, ko shakka babu, ya yi tasiri a kan haka, ba iya ’yan mazabarsa kadai ba, har ma da daukacin Al’ummar Nageriya sun anfana dashi, ta hanyoyi da dama. Inji Kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *