Ganduje ya jajantawa Kwankwaso bisa rasuwar kaninsa

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yiwa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ta’aziyya bisa rasuwar kaninsa, Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu, gwamnan ya bayyana rasuwar injiniyan da aka horas da aikin noma a matsayin rashi ba ga iyalansa kadai ba har ma da jiha da kasa baki daya.

Ya bayyana cewa marigayi Kwamared Kwankwaso ya bayyana kansa a matsayin ma’aikaci mai kwazo kafin ya yi ritaya, musamman a lokacin da ya yi aiki a shirin shukar dazuka inda ya kwashe shekaru da dama.

Gwamna

Ganduje ya yi addu’ar Allah ya jikan sa da Aljannar Firdausi da daukacin iyalansa baki daya.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *