Ganduje ya umarci ‘yan takarar APC su yi gwajin kwakwalwa akan shan miyagun kwayoyi.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya umarci masu takara da ke neman mukaman majalisar zartarwa ta APC da su yi gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi.

‘Yan takarar kansila goma sha uku a Kano sun yi gwajin ta’ammali da kwayoyi a farkon shekara.

Gwamnan ya umarci dukkan wadanda suka shiga takarar da su kai rahoton ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa a jihar domin tantance su kafin karfe 7:00 na safe.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Muhammad Garba, ya fitar ranar Laraba a Kano.

“Umarnin

yana cikin manufofin gwamnati, don kawar da Kano daga haramtattun abubuwa,” in ji Mista Garba.

Ya yi gargadin cewa babu wani dan takara da za a tantance ba tare da yin gwajin na tilas ba gabanin babban taron jihar na 16 ga Oktoba na jam’iyyar mai mulki.

Sanarwar ta kara da cewa “an gudanar da irin wannan gwajin ga masu neman shiga zaben kananan hukumomi, da kuma wadanda aka nada na siyasa ciki har da membobin majalisar zartarwa ta jihar kafin a ba su mukamin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *