Gargaɗi: Dan Allah kada wanda ya turo mun bidiyon jima’i na Tiwa Savage, domin kada a samu matsala na sume |~ Cewar Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa baya son kallon bidiyon jima’i na Tiwa Savage, dake yawo a kafafen sada zumunta.

Tsohon sanatan kuma mamba a babbar jam’iyyar hamayya PDP, yace baya son kallon bidiyon ne saboda zai iya yanke jiki ya faɗi sumamme.

Sanata Shehu Sani ya faɗi haka ne a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook, jim kaɗan bayan sakin bidiyon, kuma ya karaɗe kafafen sada zumunta.

Sani

ya ƙara da cewa a baya da ya kalli bidiyo makamancin irin wannan na jima’i, yanke jiki ya yi ya faɗi sumamme sabida kaɗuwa.

Sanatan yace: “Gargaɗi: Dan Allah kada wanda ya turo mun bidiyon Tiwa Savage, domin kada a samu matsala na sume.”

“Karo na ƙarshe da na kalli makamancin irin wannan bayan wani ya turo mun, ban san abinda ya turo ba, sai da na kwanta a gadon asibiti na kwana ɗaya.”

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *