Gidauniyar Uba sani ta dauki nauyin aikin wanda wuta ta Kona a hadarin tankar man fetir a Hanyar Abuja Zuwa kaduna.

Gidauniyar Sanatan kaduna Malam Uba sani wato Uba Sani foundation ta kai daukin ceto rayuwar Labaran Abubakar, dan shekara 19 da fashewar tankar man fetur ta rutsa dashi

Labaran Wanda ya Kasance dan rakiyar wani mai suna Musa Abdu direban tanka ne da ya cika tankarsa a Kan Hanyar Abuja zuwa Kaduna Amma tankar ta kama da wuta. An kwantar da su biyun a babban asibitin Suleja inda Musa direnan ya rasu washegarin Ranar
An kai Labaran izuwa asibitin Barau Dikko Kaduna domin jinya.

Yayin

da al’amarin nasa ya yi kamari, a makon da ya gabata aka mayar da Labaran zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika- Zariya inda za a yi masa tiyata a hannunsa sakamakon konewa da ya shafi jijiyoyin sa.

Ana haka-ana Haka ne gidauniyar Uba Sani ta samu labarin halin da Labaran ke ciki kasancewar ‘dan uwan sa, Malam Muhammad Abubakar ya gajiya da bibiyar hanyoyin da duk suka sace wajen ganin an samu damar yi wa Labaran Aikin tiyatar Amma Al’amarin yaci tura.

Shugaban gidauniyar, Sanata Uba Sani ya kawo masa dauki ta hanyar amincewa da duk kudaden da za a kashe a wajen Aikin jiyyarsa
Labaran Abubakar da kawunsa Muhammad Abubakar sun kasance cike da yabo ga Sanata Uba Sani wanda Gidauniyar sa ke aikin ceton rayuka a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da ta sa a gaba.

Idan dai ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne gidauniyar Uba Sani ta kashe sama da Naira miliyan 5 wajen gudanar da ayyukan jinya daban-daban, da suka hada da kashe kudaden majinyata masu bukatar tiyata, gwajin lafiya kyauta na masu ciwon suga, sikila, zazzabin cizon sauro da kuma hepatitis B, raba masu juna biyu kayan haihuwa ga mata daga gidajen talakawa daban daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *