Gwamna Zullum ya raba kekuna dari uku 300 ga dalibai domin samun sauƙin zuwa Makaranta.

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya raba kekunan hawa sama da dari uku 300 ga daliban da suka saba yin tattaki daga kauyukan da ke makwabtaka da su zuwa makarantun jihar.

Gwamnan ya bayar da tallafin ne a ziyarar da ya kai yankin kudancin jihar inda aka shirya gudanar da kaddamar da ayyuka 22.

Gwamnan wanda ya kaddamar da wasu ayyuka a ranakun Talata da Laraba, ya kuma kaddamar da cibiyar koyon sana’o’i da makarantar sakandare a karamar hukumar Kwaya Kusar a ranar Alhamis.

A

yayin kaddamarwar, Zulum ya sanar da tallafawa kimanin mutane 200

Ya ce, “Ya kamata a dauki sabbin malamai daga kwararru dake yankin Yimir Lang.

Ya kuma rarraba kekuna sama da 300 ga daliban da suka saba yin tattaki daga kauyukan da ke makwabtaka da su zuwa makarantu “don saukaka masu zirga-zirga Zuwa Makarantu.

A garin Ganjiwa kuma a cikin Kwaya kusar, Zulum ya jagoranci gina sabuwar makarantar sakandare ta shekarar 2022.

Kwamishinan ilimi na jihar, Lawan Abba Walkibe, ya ce, “A cikin shekaru biyu da suka wuce, gwamnatin Zulum ta gina manyan makarantu 21 masu ajujuwa 60, 30 da 20 sannan ta gina ajujuwa sama da 432 a makarantu 48 tare da gyara makarantu 39 gaba daya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *