Gwamnatin Buhari zata saka haraji kan ruwan leda ‘Pure water zai koma N50.

Kungiyar masu samar da ruwan sha ta Najeriya (WAPAN) ta bayyana cewa farashin ruwan ‘pure water’ na iya tashi daga N20 a yanzu zuwa N50 kan idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da shirin haraji kan abubuwan shaye-shaye na yau da kullum.

Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson ne ya bayyana hakan a wani taron da aka gudanar a Legas. ‘Yan Najeriya sun shaidi tashin farashin ruwa sau uku a cikin shekarar 2021; daga N5 zuwa N10 da kuma N20.

Kwamitin

Majalisar Wakilai kan Kudi a watan Agusta 2021, ya yanke shawarar cewa za ta yi wa dokar Kudi kwaskwarima don dawo da haraji kan duk wani abin sha na yau da kullum. Shugaban WAPAN na kasa, Eneri Odiri Jackson, ya ce aiwatar da haraji kan sinadarai da ake amfani da su wajen samar da ruwa zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar, kamar yadda DailyTrust ta ruwaito.

Jackson ya ce: “Babu shakka farashin pure water zai tashi daga N20 zuwa kusan N50. Ina ba da shawarar cewa gwamnati ta yi nazari hekara mai zuwa, kafin a ci gaba da aiwatar da manufar.” Kungiyar masu samar da pure water na ATWAP sun koka kan raguwar mambobi a kungiyar tasu. Mrs. Clementina Chinwe Ativie, shugabar ATWAP, ta ce mambobin kungiyar sun ragu da 16,000 sakamakon kalubalen tattalin arziki daban-daban, duk kuwa da cewa farashin pure water a kowace ya karu da fiye da 150% a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ta kuma bukaci a san yadda za a yi don a dakatar da sake dawo da haraji kan abubuwan sha.

Yunkurin dawo da harajin harajin ya fao ne daga Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Kanal Hammed Ali mai ritaya. A cewarsa shigo da abubuwan sha da ba barasa ba da kuma barasa karkashin kulawar fitar da kaya zai rage illar dogaro da kudaden harajin mai da shigo da kaya. Hakazalika, ya ce hakan zai taimaka wajen harkokin kiwon lafiya da muhalli tare da rage shan abubuwan sha masu cutarwa. Shugaban Hukumar na Kwastam ya sake nanata bukatar masu ruwa da tsaki su tattauna kan matsalolin da masana’antun Najeriya suka bayyana. Daga shafin Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *