Gwamnatin jihar Gombe ce ta ‘dauki nauyin ‘yan ta’adda domin kaiwa Sanata ‘danjuma goje Hari a Hanyar sa ta shiga Gombe ~Cewar Magoya Bayan Goje.

A jihar Gombe Bayan faruwar Rikici tsakanin magoya bayan Sanata danjuma Goje da magoya bayan Gwamnan jihar inuwa Yahaya magoya bayan Sanata danjuma Goje sun zargi Gwamnatin jihar Gombe da Kai harin ta’addanci ga tawagar Sanata danjuma Goje ‘daya daga cikin magoya bayan Goje Mohammed Muhammad Adamu Yayari ya tabbatar wa da Mikiya cewa Sanata Goje ya ziyararci jihar Gombe ne da nufin zuwa daurin aure amma Gwamnatin jihar Gombe ta turo ‘yan daba suka tare hanyar Sanatan ba tare da Sanatan ya aikata ko wanne irin laifi ba, magoya bayan Goje sun tabbatar da cewa a tawagar ‘yan daban da Suka tare Goje harda Gwamnan da kansa yaje wajen tare da DC nasa ‘yan daban sun farfasa ‘daya daga cikin motar Sanata Goje Kamar yadda yayari ya tabbatar wa da Mikiya.

A

Lokacin da Al’amarin ke faruwar A shafin sa na Facebook Mohammed adamu yayari ya wallafa labarin Yana Mai cewa da dumi dumi Yanzu haka wasu ‘yan taa’adda karkashin jagorancin Shugaban matasan jam’iyar APC na jihar Gombe Kawu Lero sun farwa Alh. Usman Muhammad Manga inda suka farfasa motarsa a bakin airport dake Lawanty. Jami’an tsaro sunyi Nasarar Kama Shugaban Matasan da Aminu Arnan Hula wanda Daya ne daga cikin Direbobin Gwamnan jihar Gombe. Inji yayari

Bayan haka yayari ya tabbatar da cewa faruwar wannan Al’amari ne yasa dubban matasa magoya bayan Sanata danjuma Goje Suka yi dandazo zuwa hanyar filin jirgin sama domin rakiya ga Sanata danjuma Goje harzuwa gidansa domin tabbatar da cikakkiyar kariya da tsaro a gare shi.

Bayan faruwar Al’amarin Sanata danjuma Goje ya bukaci matasa magoya bayan sa dasu zauna lafiya su kwantar da hankalinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *