Gwamnatin mu Kawo yanzu mun magance ‘yan ta’addan dake da alaka da ‘yan ta’addan duniya ~Cewar Lai Mohammed

A ranar Lahadi ne gwamnatin tarayya ta karyata zargin da wata kungiya mai zaman kanta mai suna Global Advocates for Terrorism Eradication (GATE) ta yi kan masu daukar nauyin ta’addanci.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Segun Adeyemi, ya fitar, ya bayyana zargin a matsayin “wani abin kyama ne da masu neman canja Maganar kan yawan hare-haren ta’addanci da ‘yan fashi da makami suke shirya.

Ta

yaya wata kungiya mai mahimmanci za ta zargi gwamnatin da ke magance muggan ta’addanci da ‘yan fashi Kuma ace itace zata dauki nauyin ta’addancin?

‘’Shin ba abin mamaki ba ne cewa wannan kungiya ta zabi wannan lokaci na musamman da ‘yan ta’adda ke mika wuya ga jama’a ko kuma suna gudun hijira sakamakon sabon farmakin da sojoji suke kai musu don shirya wani abin da zai raba hankali? Menene manufar GATE idan ba don raunana yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da Sojojin keyi ba?

GATE da masu daukar nauyinta ya kamata su ji kunyar kansu kuma su daina kokarin kawar da hankalin sojojin mu masu yin duk abin da ya kamata, gami da sadaukar da kai, don kiyaye kasarmu Zuwa ga lafiya, “in ji Ministan.

Ya ce a yakin da ake yi da ta’addanci, Nijeriya ta ci moriyar kanta, ta hanyar magance ‘yan ta’addan gida da ke da alaka da kungiyoyin ta’addanci na duniya.

Lallai Yan Najeriya ta tashi ta fuskanci kalubalen ta’addanci kamar yadda gwamnatin Buhari ta yi.
Domin zaburar da zaratan sojojin mu da kuma jagorancin shugaban kasa Muhammadu.

Buhari ya hada kai ya sanya jiga-jigan sojojin mu a wuri mai kyau domin tunkarar ‘yan ta’addan a gaba da kuma murkushe ‘yan ta’adda. Hakazalika, an yaba da kokarin Najeriya na magance ta’addanci a duniya”, in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *