Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe N8.45bn na gyaran hanyoyi a Sokoto.

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kashe kudi N8,450,829,974.95 domin gyaran hanyar Sokoto-Ilela (Nigeria) Birnin Konin (Jamhuriyar Nijar) a jihar Sokoto.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan a yau Laraba bayan taron majalisar ministocin tarayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a dakin taro na uwargidan shugaban kasa dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Ya ce kwangilar da aka amince wa Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, an ba shi ne ga Messrs Amirco Universal Concept Ltd.

Adesina

ya ce akwai takardar amincewar ginawa da kuma samar da sabon ginin Majalisar Dattawa da kuma Cibiyar Taro Ma’aikata ta Jami’ar Abuja da Ma’aikatar Ilimi ta gabatar a kan N2,354,247,466.76 ga Messrs Hilkam Engineering Consultancy Ltd.

Ya ce majalisar ta kuma amince da wata takarda da Ministan Wutar Lantarki ya gabatar na bayar da lasisin tashar samar da wutar lantarki mai karfin 400kw a cibiyar lafiya ta tarayya (FMC), Jabi, Abuja kan kudi N768,906,174.71 ga Stallion Trading and Construction Company Ltd.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *