Gwamnatin Tarayya ta Shirya Tsaf Don Rufe Shafukan IPOB na Kafafen Sada Zumuntar Zamani Wato Sohiyal Midiya.

Da alama dai amfanin da Kungiyar tsagerun haramtacciyar kungiyar nan ta yan awaren kafa kasar Biafra ya kusa ya zama tarihi, biyo bayan wani hobbasa da gwamnatin tarayya take shirin aiwatar wa don ganin ta dakile amfani da kungiyar keyi, tana haddasa rikici da kuma yada farfaganda.

Hakan ya biyo bayan wani jawabi da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osibanjo ya fitar, inda yake cewa:

Bayan rahoton da hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, Femi Adesina da Lauretta Onochie suka gabatar kan yada farfagandar da ake yadawa a kafafen yada labarai da haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB ke yadawa, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar daidaita tsarin shafukan sada zumunta da ke aiki tukuru da nufin kawo wa kasar nan mummunan suna.

class="has-text-align-justify">“Taron da aka gudanar domin kafafen yada labarai a fadar Aso Villa, ya bamu damar fahimtar abinda ke wakana domin daukan matakan da suka dace don ganin mun kawo tsari mai kyau a dandalinmu na yada labarai.

Masu yada farfagandar IPOB sun yi barna fiye da alheri a kasar nan ta hanyar karyaryaki da yaudararsu ta yau da kullum a duk fadin yanar gizp-gizo, ita IPOB din ce ta sa twitter ta goge jawabin shugaban kasa kuma idan aka kyale hakan to Nijeriya za ta zama kasa ta farko da babu doka da oda a kasa.

Ina godiya ga masu taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu, Femi Adesina da Lauretta Onochie bisa irin wannan shawara da shawarwari kuma mun yi alkawarin yin aiki dasu cikin gaggawa, za’a sanar da mai girma ministan sadarwa ya bibiyeta, tare da duk wasu shafukan sadarwa da ke aiki a Najeriya.” Inji Farfesa Yemi Osibanjo, mataimakin shugaban Najeriya

Rahoto: Abubakar Mustapha

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *