Har’ila yau wasu Jiga-jigan Siyasa ‘yan kasuwa da Mata da matasa daga Jihar kebbi sun bukaci Gwamna Yahaya Bello ya fito takarar Shugaban kasar Nageriya.

Wasu tawagar Jiga jigan ‘yan siyasa, Yan kasuwa, matasa da samari daga jihar kebbi sun Kai ziyara ga Gwamna Yahaya Bello na Kogi a kokarin su na Kai jinjina da ban girma a gareshi a matsayinsa na matashi baya da Haka Kuma tare da mika buqatar domin ya fito ya nemi kujerar shugaban kasar Nigeriya
Matasan sun Sha alwashin Goya Masa baya idan harya amshi kiransu ya tsaya takarar Shugaban kasa a zaben 2023 Mai Zuwa.

A

karshen sunyi addu’ar fatan Alkhari ga Ga jajirtaccen Gwamna tare da mika Kai ga Allah domin Kasancewar Mulki na Allah ne Kuma a wajensa ake nema.

Gwamna Yahaya Bello na kogi ya Kasance sahun gaba-gaba wajen tallafawa Al’umma musamman matasa a duk fa’din Tarayyar Nageriya.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *