Haryanzu bamu tabbatar da ko waye Shugaban Jam’iyar APC ba a Jihar Kano ~Cewar Uwar Jam’iya.

Daya daga cikin’yan kwamatin riko na uwar jam’iyyar APC ta kasa, kuma shugaban matasa na kasa Ismail Ahmed ya bayyana cewar har yanzu uwar jam’iyyar APC ta kasa bata kai ga ayyana waye sahihin shugaban jam’iyya a Kano ba.

Ismail Ahmed ya bayyana haka ne ga gidan Radiyo Freedom dake Kano a zantawarsa da Nasiru Salisu. A cewarsa uwar jam’iyyar zata yi nazari sannan ta fadi matsaya akan shugabancin Jam’iyyar reshen jihar Kano.

A

karshen makon jiya ne dai aka samu bangarori guda biyu masu hamayya da juna na ikirarin sune halastattun shugabannin jam’iyyar bayan da kowanne yake ikirarin an zabe shi tsakanin bangaren Abdullahi Abbas dake tare da Gwamnatin Kano, da kuma bangaren Danzago da suke tare da Sanata Ibrahim Shekarau.

–Daily Nigerian

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *