Hatta zazzabin yau da kullum yafi CoronaVirus kashe Jama’a to don me zan kulle Jama’a ta kan wata COVID-19? ~Cewar Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi gargadin cewa masu aikata laifuka suna amfani da abin rufe fuska da nufin dakile yaduwar COVID-19 suna yin hakan ne kawai domin boye sunayensu da yin fashi a wuraren taruwar jama’a.

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya ranar Juma’a a wajen liyafar karramawar da aka yi na karrama wakilan kafafen yada labarai na Najeriya a Lokoja, babban birnin jihar.

Ya yi ikirarin cewa an cuso COVID-19 a Najeriya, bayan cewa ‘yan Najeriya na fama da cututtuka fiye da kwayar cutar COVID-19

Ya

ce, “Hakika, masu laifi suna amfani da abin rufe fuska don suturta kansu. Suna rufe fuskokinsu sukan sauka a otal domin zuwa wuraren aikata Laifin su don haka ba za ku iya gane su ba.

“An fahimtar da ni cewa coronavirus bata kai kashi ɗaya cikin ɗari ba; hatta zazzabi na yau da kullun ya fi coronavirus sawawa mutuwa.

Bello, wanda ke amsa tambayoyi daga ‘yan jarida game da matsayar sa kan annobar COVID-19 a Najeriya, ya ce gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai don wayar da kan mazaunanta wajen kula da tsaftar bil-adama a muhallin su.

Ba zan kulle mutane na ba saboda coronavirus saboda mun sami bullar wasu cututtuka masu hatsari a fiye da ita a jihar Kogi.

“Muna da zazzabin Lassa, muna da zazzabin Yellow, kuma mun sami nasarar shawo kan duk wata Matsala a jihar Kogi ba tare da matsawa Jama’a ba To don me zan kulle mutanena?”

“Kulle mutanenmu zai kawo illa mai yawa; yana iya zama Babbar Matsalar tattalin arziki, za a sami tasirin tsaro; hasali ma yana iya haifar da cin hanci da rashawa”. Inji yahaya Bello.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *