Hukumar EFCC rashen jihar sokoto ta damke wasu mutum biyu da suka jima suna damfarar mutane da sunan Samar musu aiki.

Hukumar EFCC reshen jihar Sokoto ta sami nasarar kama wasu masu damfara mutane.

Hukumar EFCC rashen jihar sokoto ta damke wasu mutum biyu da suka jima suna damfarar mutane da sunan Samar musu aiki, wadanda aka kama sun hada da Ibrahim Shehu da John Danjuma, saboda tuhuma akan wata badakalar samar da aiki, hadin baki da karbar kudi ta hanyar yaudara kimanin naira miliyan daya da dubu dari da sittin.

Ana

zargin mutanen biyu ne da hadin baki tare da yaudarar wasu da basu jiba basu gani ba cewa suna da guraben aiki a hukumar shige da fice ta kasa na siyarwa.

Bincike ya nuna karya ne kawai suke yi ba bu wani gurbin aiki a hukumar.

Daya ke gabatar da su a gaban Manema labarai shugaban Hukumar Reshen jihar sokoto ya bayyana cewa Hukumar tana kan buncike, Kuma da zaran ta kammala bincike zata gabatar dasu gaban kotu.

Daga murtala ST Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *