Hukumar ‘yan sanda ta dakatar DCP Abba Kyari bisa dogaro da labarin yanar gizo-gizo a daidai lokacin da Kuma Nageriya ke fama da matsalar ta’addanci…

Wato a Jiya nasha mamaki a daidai Lokacin da na tsinci wata sanarwa daga shugaban rundunar ‘yan sandan Nageriya IG Usman Alkali Kan batun dakatar da DCP Abba Kyari da rundunar ‘yan sandan tayi a wattanin da suka gabata a baya, inda shugaban ‘yan sandan yace lamarin Abba Kyari haryanzu basu karbi wata takardar bukata daga hukumar ta FBI ba, su kan su rundunar ‘yan sandan Nageriya a yanar gizo-gizo Suka tsinci labarin wannan badakalar kamar yadda jarida Whithing Nigeria ta ruwaito.

Muna

sane da yadda lamarin badakalar DCP Abba Kyari da Abbas Hushpuppi ta karade kafafen sada zumintar zamani na gida Nageriya dama sauran kasashen ke tare Kan cewa Shugaban na rundunar ta IRT DCP Abba kyari ya karbi rashawa daga hannun shahararren ‘dan damfara Hushpuppi bisa wata sanarwa da hukumar FBI dake kasar amurka aka ce tayi.

Lamarin da ya ja hankulan yan Nageriya yasa Sukayi ta CeCe kuce, hakan yasa hukumar ‘Yan Sanda ta dakatar da DCP Abba Kyari.

Wato ni abin tambayata da mamaki shine ace kasa mai girma da daraja Mai ‘dauke da kima a idon duniya kamar Nageriya ce zata ‘dauki wannan danyen hukunci haka nan take? Daga Mun samu labari kawai a yanar gizo gizo sai Kuma muyi aiki dashi mu hukunta kan mu da kanmu?
‘dan sanda mai matukar kokari wanda duniya ta shede shi wajen kare martaba da kimar rayuwar ‘yan Nageriya shine zamu dakatar dashi kawai bisa dogaro Kan batun da muka tsinta a yanar guzo-gizo a daidai Lokacin da muke fama da matsalar kalubalen tsaro? ‘dan sandan da yayi kaurin suna wajen tarwatsa rundunar ‘yan ta’addan masu garkuwa da mutane wanda duniya ta sheda hakan shine zamu ajiye a gida a wañnan Lokacin na mummunan matsalar tsaro da muke fuskanta?

Karku manta shine shugaban runduna ‘daya tilo da majalisar wakilan Nageriya ta sheda Kuma ta aminta da aikin sa hakan yasa majalisar ta Kira shi ta bashi lambar yabo.

Shine ‘dan sandan da matar shugaban kasa Aisha buhari ta karrama da lambar yabo.

Kai hatta ita hukumar ta FBI dake kasar amurka sai da ta bashi lambar yabo domin jajircewarsa Kan yaki da ta’addanci.

Maganar gaskiya bamu shirya mu zauna lafiya ba nageriya.

Duk da haka a karshe Muna Kira da shugaban hukumar ‘yan sandan Nageriya IG Usman Alkali da sauran masu fa’da aji da su yi fatali da wannan shirme na yanar gizo-gizo su dawo Mana da shugaban rundunar ta IRT DCP Abba Kyari domin cigaba da aikin sa na Sadaukar da Kai ga kasarmu Nageriya Nageriya Mai albarka domin kawo karshen ta’addancin ‘yan ta’adda, marubucin wannan makala shine Inuwa Hamisu…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *