Hukuncin dandaka ne ya dace ga masu aikata fyade ga mata ~Cewar Ministar matan Nageriya.

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Jagororin Shugaba Muhammadu ta bakin Ministar harkokin mata da ci gaban jama’a Pauline Tallen, ta yi kira da a yi amfani da dandaka a matsayin hukunci gamasu aikata laifin fyade a fadin kasar nan.

Ta yi wannan magana ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a wani bangare na ayyukan karbar bakuncin babbar daraktar asusun kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya, Natalia Kanem, wacce ta ziyarci kasar ta Najeriya.

Ministar

wacce ta bayyana yin dandaka a matsayin hukuncin da ya fi dacewa ga masu laifin, ta ce yin hakan shine hanyar da za’ayi amfani da ita wajan tozarta masu laifin Kuma zai rage barazanar samun masu Aikata Fyade.

Ta Kuma Kara da cewa: “Wannan shi ne laifi mafi muni ga kowane yaro ko yarinya Ba yaron ko yarinyar kawai ya sami mummunan rauni ba, kuma za ta rayu tare da shi har abada. Uwar kuma za ta ci gaba da kasancewa cikin rashin jindadi a duk rayuwarta kuma saboda haka, muna ba da shawarar a yanke hukunci mai tsauri kan irin waɗannan lamuran na Fyade.

“Idan muka yi daya ko biyu, na yi imani babban laifi nau’in lalata da fyade zai ragu, don haka ne muke dagewa cewa duk jihohi dole ne su yi amfani da dokar VAP, da dokar kare hakkin yara, amma ba wai kawai a samar da ita ba ne kawai, sai an tabbatar da aiwatar da ita.”

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *