Inaso na auri mahaukaciya, shashatau kuma shagira salon girbau, Indai iyayenta zasu cilla min ₦500,000 a asusun ajiya na na banki kuma zasu kula dani da ita – Matashi.

Idan da ranka zakasha kallo, ka more har ka gaji.

Wani faifan bidiyo ya bayyana kuma ya karaɗe shafukan sada zumunci na zamani wato yanar gizo wanda ke nuna wani mutum yana bayyana cewa yana son yin aure ga mahaukaciya idan har iyayen ta zasu kula da shi.

A cikin faifan bidiyon, an ji mutumin daya bayyana sunan sa da Denis Nonso yana faɗar ainihin sunayensa, daga ina ya fito da kuma dalilin da ya sa yake son ya auri mara hankalin idan ansamu.

class="has-text-align-justify">Ya bayyana cewa akwai wasu attajirai masu irin wannan ƙalubalen yara, kuma zai yarda ya auri ɗaya, matukar za a fara biyan sa N500,000 a cikin asusun banki kuma idan iyayenta ma sun yarda su kula da shi da matar tashi, yana kwance ya dinga jan girki ɓagas abinsa.


Kawo yanzu dai babu wani shahararren mai kuɗi daya nuna sha’awar aura wannan mutumin diyarsa mahaukaciya ko shashatau, amma da alama abin dayake bida ya kawo kace nace a kafafen sada zumunci na zamani.

Ku latsa domin kallon vidiyon:


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *