IPPIS : Jami’o’in Najeriya Suna Sakamu Muna Biyan Albashin Malaman Da Suka Mutu – Akawunta Janar.

Daga Miftahu Ahmad Panda

A Jiya Litinin ne Gwamnatin Tarayyar Kasarnan Ta Bayyana Cewar Hukumomin Jami’o’in Kasarnan Suna Saka Gwamnatin Biyan Albashin Malamai Membobin Kungiyar Da Suka Rasu Ta Hanyar Yin Amfani Da Hadadden Tsarinnan Na Biyan Albashin Bai Daya (IPPIS),

Akawunta Janar Na Gwamnatin Tarayya, Ahmed Idris ne Ya Bayyana Hakan, Inda yace Gwamnati Zatayi Kokarin Kawo Karshen Biyan Kudin Albashin Da Gwamnati take baiwa Malaman Jami’o’in Kasarnan Da Suka rigamu Gidan Gaskiya, Duba da Rufa – Rufa Tareda kin Bayyana Rasuwar tasu Da Kungiyar Malaman Jami’o’in takeyi,

Gwamnatin

Tarayyar Dai Ta zargi wasu daga Cikin Hukumomin Jami’o’in Kasarnan Da Tura Mata Jadawalin Malaman Da Za’a biya Albashi wanda Jadawalin ya hadarda Malaman Da Suka Rasa Rayukansu.

Idan Baku Mantaba Dai tuni Kungiyar Malaman Jami’o’in Ta Kasa (ASUU) Ta Tsunduma Yajin Aiki Domin Nuna Kin Gamsuwarta Da Wannan Tsari Na Biyan Albashin Bai Daya (IPPS) dakuma kin Biyansu Albashi Da Gwamnatin Tarayya Tayi, Wanda Daga Bisani Gwamnatin Ta biya Malaman Jami’o’in Albashinsu, Amma Har Yanzu Gwamnatin Ta Tarayya batakai Ga Cimma Yarjejeniyar Da zatasa Kungiyar Ta ASUU Ta Kawo Karshen Yajin Aikin Da Ta Tsunduma ba, Sai gashi kuma Wannan Zargi ya fito daga Gwamnatin Ta Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *