Jam’iyar APC ta dawo kan ganiyarta sannan mutane suna tururuwar shiga cikinta- Buhari

JAM’IYAR APC TA DAWO KAN GANIYAR TA, CEWAR SHUGABA BUHARI, SANNAN YA TAYA MEMBOBIN KWAMITIN RIKO MURNA KAN GUDANAR DA AIKI MAI KYAU.

Shugaba Muhammadu Buhari ranar Juma’a a Abuja yace, Jam’iyar APC ta Farfado ta kara karfi da sake matsaya kan Babban taron kasa da zabe dake tafe nan gaba, yayin kuma daya Jinjina wa Babban Kwamitin Riko da Shirya Babban taron Jam’iyar na Ƙasa karkashin Shugabancin Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.

Da yake magana a Gurin taron Babban Kwamitin Riko da Shirya Babban taron Jam’iyar na Ƙasa a Fadar Shugaban Kasa, Shugaba Buhari yace akwai haske cikin Sa’a da Jam’iyar keda shi ta hanyar sake tattara da Sulhunta membobin Jam’iyar a kasa baki daya, Shugaban yace “Saboda aikin da Kwamitin ya gudanar Jam’iyar ta sake dawo kan ganiyar ta.”

“Cikin

Shauki na saurari irin gagarumin aikin da kawo yanzu kukayi,” a Cewar sa. “Dukkan mu shaida ne kan Rikicin da Jam’iyar ta auka ciki wanda yayi sanadin kaiwa kararraki da nuna son kai da banbance banbance cikin Jam’iyar.”

Shugaba Buhari yace, tsari Jam’iyar ya sabo matsala saboda Rikice Rikice wanda yayi ta ci gaba da kunnuwa har ya bada dama yin zabe daban daban, ya lura cewa yanzu Babban Sakatariyar Jam’iyar ya dan numfasa nayin yin aiyuka cikin lumana bayan da aka samu Sulhu.

Shugaba Buhari ya fadawa Membobin Kwamitin cewa zasuci gaba da samun goyon bayan dukkanin Manyan Kutsoshin Jam’iyar domin kammala aiki da akan basu na shirya Babban taron Jam’iyar na Ƙasa da barin “Gurbi wanda zai kafu daram.”

Shugaban ya kara da cewa “Muna so mu bar tarihi mai kyau na Gaskiya da Adalci, wanda abinda Jam’iyar ke bukata kenan don ta tsira,”

Cikin Jawaban sa, Shugaban Kwamitin Riko da Shirya Babban taron Jam’iyar na Ƙasa, yace Kwamitin ta tsunduma aikin ne da kokari da sadaukarwa don ceto Jam’iyar daga rugujewa.

Gwamnan na jihar Yobe ya shaida cewa dukkan Matsalolin da Membobin su an musu Adalci Gurin sauraren su, da samar da tsari rashin rufa rufa domin bada masauki ga dukkan wa’anda suka fusata, wanda hakan ya sanya suka janye karar da suka shigar a kotu da fahimtar juna cikin ruwan sanyi.

“A halin yanzu mun samu ana ta tururuwan shiga Jam’iyar tamu, ciki harda Gwamnoni daga Jam’iyar PDP.

“Yanzu Jam’iyar tafi zama a halin lafiya, daidai tuwa da samar da Gurin zama fiye da yadda muka samu a kasa. Dukkan da farko akwai barazana, sake tallatar da Wayar da kai ya bamu damar kawar da tsoron dace zukatan Membobin,” Cewar Gwamna Buni.

Gwamnan na jihar Yobe yace, An samu Membobin Jam’iyar sama da Miliyan 40 da suka yanki katin Jam’iyar da kuma wanda suka sabunta katin nasu a kasa baki daya, kuma an kafa Kwamitin na miƙa Ƙorafi wanda zai saurari dukkan wasu Matsalolin da suka shafi aikin don kada a samu wani memba ko guda da aka tauyewa hakki.

Gwamnan ya kara da cewa “Mun fahimci cewa Matasa da Mata sun bada akasarin yawan da zasu kada mana kuru’a. Muna da Kwamitin na Matasa da Mata, dama kuma Mutane masu dauke da nakasa,

Yace, an kuma kafa tawagar Tuntuba da Shirya dabaru a kowace jiha don tazo da wani tsari karɓaɓɓe wanda zai tabbatar da Yin Adalci da gamsuwa da amintuwa da Shirya tsarin zabe na cikin Jam’iya.

Buni ya kuma ce, Kwamitin ta kafa tsari dazai kara duba Dokar Jam’iyar da gane mana guraren da ke janyo rashin fahimta tsakanin Membobi, wanda yanzu tuni an samu yarjenoniyoyi sama da 500.

Shugaban Kwamitin Riko da Shirya Babban taron Jam’iyar na Ƙasa, ya fadi wa Shugaban kasa da Sauran Membobin Jam’iyar cewa Membobin Jam’iyu sama da 14 sun nuna bukatar su na neman tsayawa takara a Zaben Gwamnan jihar Anambra. Ya bada tabbaci cewa Zaben fidda gwani na Jam’iyar zai gudana cikin gaskiya da Adalci.

Gwamnan na jihar Yobe yace, sun gani kudi mai yawa mallakin Jam’iyar, kuma Kwamitin yayi aikin da Membobin don biyan dukkan wasu bashi, bayan kammalawa, ya nuna cewa an kammala biyan kudin Babban Sakatariyar Jam’iyar APC.

Ya kara da cewa “Membobin Jam’iyar sun amince a sanya wa Sakatariyar suna da Gidan Muhammadu Buhari

Yayin daya godewa Shugaban kasa kan goyon baya daya basu da sanya ido kan yadda aikin su ke gudana, Gwamna Buni ya nuna cewa an gudanar da taron kasa na Matasa Membobin Jam’iyar wanda wani Bangaren na fara karfafa Jam’iyar daga tushe da tabbatar da dacewar dukkanin masu ruwa da tsaki.

Wasu daga cikin Membobin Jam’iyar APC da suka halarci taron sun kunshi, Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyar APC Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Gwamnan Jihar Filato Simon Bako Lalong.

Saura sun hada da, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da Gwamnan Jihar Osun Adegboyega Oyetola da Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani Bello.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *