Jihar Ribas ta rufe wani allon talla mai nuna faifan bidiyon wajoko akan titi.

Hukumar kula da tallace tallace ta jihar Rivers wacce aka fi sani da suna RISSA, ta kama wasu ma’aikata guda biyu na wani kamfani mai sana’ar tallace tallace ta hanyar nuna faifan bidiyo a wuraren dake haɗa jama’a.

Hukumar ta kama masu kamfanin ne a yayin da na’urorin su na faifan bidiyo da suke nuna wa don talla, ya nuna wasu marasa ɗa’a tsirara suna wajoko a yankin Garrison, dake can jihar ta Rivers.

class="wp-block-image size-full">

A ranar 14 ga watan Oktoba na shekarar 2021 ne dai da daddare, suka haska wa mutane faifan bidiyon mai daƙiƙa 60, kafin daga bisani kuma su cire.

Shugaban hukumar na riƙon ƙwarya, Tony Okeah, yace zasu gudanar da bincike akan kamfanin, sannan zasu tura su kotu da zarar ƴan sanda sun gama bincike.

Amma yanzu zancen da akeyi, hukumar ta daɗe da garƙame allon da yake tallan, tunda ya haddasawa mutane tashin hankali da kuma fusata masu tafiya.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *