JIN-JINA: Dakarun sojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 70 cikin mako guda, sun kama mahara 34.

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa rundunar ‘Operation Hadarin Daji, Whirl Stroke, safe haven da Punch/Thunder’ sun kashe mahara 70 a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a cikin makonni biyu.

Darektan yada labarai na hedikwatar Bernard Onyeuko ne ya sanar da aka a Abuja ranar Asabar da yake bayyana namijin kokarin da dakarun sojojin suka yi na ganin an ga bayan mahara daga tsakanin ranakun 17 zuwa 30 ga Oktoba.

Ya

ce ‘Operation Hadarin Daji’ ta dauki tsauraran matakai wanda hakan ya taimaka wajen fatattakar ‘yan bindiga dake jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina da Kaduna.

Ya ce a tsakanin wadannan ranaku dakarun sun ceto mutum 15 da aka yi garkuwa da su, sun kashe mahara 9 sannan sun kama wasu mahara 34.

“Dakarun sun kwato manyan bindigogi kiran AK47 guda 11, tsabar harsasai 43 da dabobi 86.

Ya ce rundunar ta damka maharan, kayan da suka kwato da mutanen da suka ceto hannu ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.

Daga nan Onyeuko ya ce ‘Operation Whirl Punch/Thunder’ sun yi arangama da wasu ‘yan bindiga a yankin jihar Kadun kuma sun kashe da dama daga cikinsu.

Ya ce dakarun sojojin sun kashe mahara 12, sun kwato manyan bindigogi kira AK47 guda 11, tsabar harsashi 64 da dabobbi 24.

Jiragen sama na yaki sun taimaka wajen kashe wasu mahara 50 a yakin Saulawa zuwa Farin Ruwa dake karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

“Dakarun sojojin sun samu wannan nasara ne a dalilin binciken sirri na hikima da rundunar ta gudanar inda ta gano cewa maharan sun dana wa sojojin dake ƙasa tarko domin su gama da su a wadannan wurare.

Bayan haka ‘Operation Safe Haven ta kama bata gari 8 sannan sun kwato bingigogi 13, harsashai 291 da dabobin mutane da aka sato 28 a jihar Filato.

Rundunar ta kuma yi zama da sarakunan gargajiyan yankin da suka fi fama da barkewar rikici domin sassan ta su.

Daga karshen rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ ta kama mahara 11 sannan ta ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su daga jihohin Benue, Nasarawa da Taraba.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *