Ka cire tsoro ayi Abinda ya dace, Aisha Buhari tayiwa Pantami Habaici Kan bidiyon kukansa a masallaci.

A wani sako Uwar gidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta wallafa wani faifan bidiyo na Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami a Lokacin da yake kuka a wani wa’azi da yake gabatarwa a Masallacin Annur dake Abuja, ta rubuta ‘A cire tsoro ayi abinda ya dace’.

Aisha Buhari ta wallafa wannan sako ne a shafinta na Instagram.

Ko me take nufi da hakan?

Idan

mukayi sharshi tare da tuna Abubuwan da Sheikh Pantami yayi a Lokacin mulkin wasu Shugabanni na baya zamu iya cewa uwar Gidan Shugaban kasar tana yiwa Pantami Habaici ne Kan yadda ya Kasance yanxu bashi iya fadin Gaskiya a wannan Gwamnati kasancewar yanzu Yana cikim Gwamnati, idan baku manta ba Pantami ya shahara wajen kuka tare da kalubalantar Gwamnati musamman Acikin wa’azinsa ko Kuma al’kunut a Cikin Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *