Ka Gaggauta dawo da Twitter a Nageriya ~Sakon SERAP ga Buhari

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa (SERAP) ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya “gaggauta janye sharuddan dakatar Twitter har zuwa lokacin yanke hukunci na karshe a kotun shari’ar ECOWAS a Abuja da ke kalubalantar hakin dakatarwar ta Twitter, SERAP ta bukaci Hakane domin bawa kotu damar yanke hukunci kan muhimman batutuwan da ke cikin shari’ar, da kuma kare hakkoki da muradun masu shigar da kara. ”

Shugaba Buhari ya bayyana a cikin jawabinsa na murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai, cewa gwamnatin tarayya za ta dage dakatarwar da aka yi wa Twitter a Najeriya ne kawai idan an cika wasu sharudda, ciki har da damuwa game da tsaron kasa. Hakanan Kuma jawabin yana nuna cewa ko da an cire dakatarwar, za a ba ‘yan Najeriya damar amfani da Twitter ne kawai “don kulla kasuwanci da kyawawan Ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *