Ka hanzarta ceto nagartar ka, wadanda ka yarda da su ke ‘batar da kai, domin ba su da manufa irin ta ka, |~ Dalung ya fada’wa Buhari

Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya ce tsohon ubangidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama da matsalar bacin suna saboda wadanda ya yarda da su ba su yin abinda ya dace.

Dalung, wanda ya yi aiki karkashin Buhari a matsayin minista daga 2015 zuwa 2019, ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya yi kira ga shugaban kasar da ya gaggauta kai wa nagartarsa dauki.

Ya kara da shawartar shugaban kasan kan ya sani cewa nagartarsa kadai ba za ta iya ceto kasar nan ba matukar wadanda ya bai wa mukamai suna yin abinda bai dace ba.

Wani

sashi na wallafar ta ce, “Idan kowa na sauke nauyin da ke kansa cike da gaskiya, tabbas gaskiyar halinka da dabi’un ba za su bayyana ba ma tun farko.

Tunda ya dogara da su wurin mulki, labaransu gaskiya ne a wurin ka wanda kuma akasin hakan ne a bayyane.

“Kalubalen shugabanci sun ci galaba a kan ka da kuma tsananin bukatar taimako, amma abun takaicin shi ne yadda ka ke zagaye da mutanen da manufar ku ba daya bace ba.”

Dalung ya ce shugaban kasa ya dace ya sani cewa, ba zai iya sauke nauyin da ke kansa na shugabancin kasa shi kadai ba saboda yawan abinda ke gabansa.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *