KADUNA: Ƴan bindiga sun soma karɓar dafaffen abinci a matsayin kuɗin fansa.

Duniya juyi juyi, yanzu haka ƴan bindigar

dake yankin Birnin Gwarn jihar Kaduna sun soma amsar dafaffen abinci a madadin kuɗin fansa dasuka saba tambaya.

Rahotanni sun suna cewar, ayyukan da yan bindigar ke yi a yankin yayi matuƙar ja dabaya, biyo bayan doka da gwamnatin jihar ta saka, wacce tahana cin kasuwar mako mako da akeyi.

Babangida Yaro shugaba ne na matasa a yankin, ya shaidawa jaridar Aminiya cewa, yanzu haka ƴan bindigar da zarar sun kama maka mutum, bazasu tambayi kuɗi ba sai dai dafaffen waku, wato abinci.

class="has-text-align-justify">Bugu da ƙari, ya shaidawa majiyar tamu cewa, dokar hana Saida man fetur da akayi, yayi matuƙar nakasa zirga-zirgan maharan a yankin.

A cewar sa:

“Yanzu an fara samun zaman lafiya a Damari, Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindiga sun daina kai mana hari. Yanzu sun fi maida hankali wajen kwace dafaffen abinci musamman a wajen ‘yan talla,” inji shi.

A faɗar sa, idan masu garkuwa da jama’a yanzu suka kama mutum uku, sukan saki mutum daya ne yaje gida ya amso musu kudin fansa, tunda babu hanyar da za’ai amfani da ita wajen sadarwa.Babangida ya kara da cewa, dokar hana hawa babur ya ƙara jefa ƴan bindigar acikin halin laila-ha-ula-i.

Sai dai yace, yankin nan na “Dogon Dawa” dake jihar ta Kaduna, har yanzu yana fuskantar ƙalubalen ƴan bindigar, domin har yanzu ƴan yankin basa iya fita zuwa gonakin su.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *