Kai jama’a: Ganin ƙwaƙwaf a wayar miji, ya cilla wata mata gidan yari.

Haƙiƙa tsautsayi dai baya wuce ranarsa. Tabbas, wannan haka yake idan akayi la’akari da yadda wata idan aka yi la’akari da wannan mata data yankowa kanta katin zama a gidan cin gabza, biyo bayan habzi da tayi da wayar mijin ta batare da izinin sa ba.

Shin yaya aka haihu a ragaya?

Biyo bayan ɗaukar wayar tasa ne ba bisa izini ba, mijin matar ya maka matar tasa a wata kotu, inda yake zargen ta da duba wayarsa ba tare da izininsa ba, sannan ya buƙaci kotun ta bi masa haƙƙin sa.

class="has-text-align-justify">Bugu da ƙari, mijin matar ya tuhume ta da kwafar bayanai, hotuna da tattaunawarsa da wasu abubuwan ta wasu manhajoji.

Bayan da aka gudanar da zurzurfan bincike ne dai, kotun da ke yankin Ras a Al-Khaima ta sami matar da laifin keta sirrin mijin nata. Bayan wata uku a gidan yarin, kotun ta kuma yanke wa matar hukuncin biyan tarar kudi dinar 8,100, bayan.

To amma fa duk da haka, matar ta nace akan cewa ita fa tana zargin mijin nata da cin amanarta ne, wanda shi ne ummul-aba’isin da ya sa ta har takai ga bincikar wayar tasa.

Idan dai ba’a manta ba, ƙasar Daular Larabawa dai ta yi matuƙar ƙaurin suna wajen kafa dokoki masu tsauri, musamman wanda suka shafi sha’anin aure da zamantakewa al’umma. Yanzu dai wannan a kotun ta Hadaddiyar Daular ta Larabawa (UAE) tasa jami’an tsaron gidan gyaran hali sun angiza ƙeyar wannan mata zuwa gidan yarin, biyo bayan yanke mata hukuncin ɗaurin wata uku a kurkuku saboda duba wayar mijinta, ba tare da izininsa ba.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *