Kalaman batanci a Facebook Kotu ta tura wani sarki zuwa gidan Yari a jihar Nasarawa.

Rahotonni daga garin mararaban Abuja da jihar Nasarawa na cewa a jiya Ranar Alhamis wata kotun Upper Area Court dake zamanta a Garin na Maraba ta tusa keyar wani sarki zuwa gidan Gyaran Hali dake garin keffi na Jihar Nasarawan bisa zargin laifin bata suna a shafin sada zumintar zamani na Facebook mai shari’a Alkali Abubakar tijjani ne yayi wannan umarni da cewa a Kai sarkin gidan yari na tsawon kwana ‘daya ma’ana Yau ranar juma’a 17/11/2021 domin dawowa kotu a cigaba da shari’a Alkalin ya bayar da wannan Umarni ne bayan lauyoyi sun tafka muhawara a gaban sa.

Sarkin

na hausawan marabar Gurku Alh Usman adamu Mani ya kwana daya a gidan yari tare da haruna bala mai magana da yawunsa na Facebook.

Wani ‘dan kasuwa ne mai suna Alh Sani Ahmad zangina ya maka Sarkin a kotu bisa zargin sarkin yayi amfani da mai taimaka masa a shafin Facebook wato haruna Bala domin ya’da kalaman batanci da cin zarafi ga ‘dan kasuwar tare da mahaifinsa wanda hakan yasa ‘dan kasuwar daukar matakin shari’a kamar yadda ya bayyana wa majiyarmu.

Yanzu haka dai sarkin na fuskantar shara’o’i uku wanda Kuma duk Sani Ahmad zangina ne ya shigar dashi bisa zargin bata suna.

A watan nuwamba daya gabata idan baku manta ba mun labarta maku yadda wani Alkalin Kotun majistiri ta ‘daya Mai suna Theophilus lama ya bayarda umarni ga Jami’an ‘yan Sanda Kan Cewa a kamo sarkin bayan sani Ahmad zangina ya shigar da Kara gaban kotun domin tuhumar sarkin Kan sharin bata suna da jefa kalmar ta’addanci ga ‘dan kasuwar tare da mahaifinsa sai dai a daidai Lokacin da Jama’an ‘yan sanda Suka Isa ga fadarsa sarkin ya Tabbatar da Cewa yafi Karfin a kamashi domin shi sarki ne Kuma Yana da Jama’a sama da mutum Bilyan biyar 5b (FIVE THOUSAND MILLIONS PEOPLES) a ƙarƙashin sa.

A Karshe sarkin ya ce sai dai a kawo masa sammaci amma ba zai aminta a kamashi ba idan Kuma aka matsa masa zai Kira shugabar alkalai ta jihar Nasarawa.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *