KALLO YA KOMA SAMA: Wani Uba ya ɗauki ƴarsa, ya kaita daji, sannan ya kashe ta, saboda wai baƙa ce, shi kuma fari ne.

Wani mahaifi ya kashe ƴar sa mai suna Aisha da akafi sani da suna “Maulida”, yarinya mai shekaru 16 a duniya. Bayan ya ɗauke ta a adaidaita sahu, sun fita gida, sai ya dawo babu ɗiyar tasa.

Zulai Muhammad, itace uwa ga Maulida, ta bayyana yadda hakan ta faru:

Babanta ya ɗauke ta, sun fita, amma basu dawo ba, shi ya kwana, itama ta kwana, sai washe gari ya dawo. Daya dawo, isansa ko sallama baiyi ba, ya fara tambaya ina Maulida, akace masa bakai ka fita da Maulida ba, ai in tambaya ne, mu zamu tambaye ka.

Sai yake cewa wai shi ya sauke ta a bakin kasuwa, ya siyi kifi ya bata ta dawo gida. Yadda shi mutumin yake gaya min kenan“.

“Daman kuma kafin haka ya faru, ranar laraba, yayi mata duka, yace zai kashe ta, yana sunanta, ya shaƙe wuyan ta, ta cije shi, sai ya sake ta”. Inji mahaifiyar Maulida.

Cikin jimami Zulai Muhammad ta bayyanawa yadda ta samu labarin mutuwar ɗiyar tata, da yadda akayi ta gane cewa, ƴar ta ce gawar da aka tsinta:

An ce min anga gawa, aka dauko hoton aka kawo mini, akace nagani ko ƴata ce? Ko ba ita bace. Dana kalla naga ƙafanta , anan na gane itace, da kuma hannunta, da kuma warwaron data sa, da zoben data sa.”

Zulai Muhammad ta ƙara da cewa:

Ni nasan mahaifin yarinyar zai iya aikatawa, saboda zamantakewa na dashi, a lokacin da muna tare, ba zaman lafiya, duk abinda ya shafi haƙƙin aure baya mini, kuma idan nayi magana, sai ya buge ni a kaina, kuma abu kaɗan ya dinga dukanta, yace zai kashe ta“.

Wannan al’amari dai, ya faru ne a Mayo Balwa dake can jihar Adamawa, tuni dai Ƴan sanda suka cika hannu da mahaifin Maulida, wato Muhammad Saleh, ɗan shekara arba’in 42.

Ga abinda yake cewa:

“Na kashe ƴata ne, saboda maman yarinyar tace ba ƴata bace, tazo da cikin ne. Ya daɗe Sosai, kimanin shekarun ta ita yarinya 16“.

Yadda akayi na kashe ta:

Tunda na haife ta, maman tace tayi baƙa, wai anyi anyi anyi a zubar da cikin abin ya gagara, lokacin cikinta.”Shine aka bani ita na aura, mamanta da kanta ma ta gaya mini, tace mini, yarinyar nan na kalli goshinta, Ni fari sol nake, ita kuma baƙa ce. Wannan ba ƴa ta bace”.

DSP Yahaya Ngroje shine mai magana da yawun ƴan sanda na jihar Adamawa, yace:

Yanzu dai har ila yau, ana matakin gudanar da bincike domin dole mu samu shaida daga likitoci waɗanda zasu tabbatar mana da ita gawar macece. Abinda zamu tabbatar wa al’umma, zamuyi iya ƙoƙarin mu domin yin wannan bincike a cikin kankanin lokaci kuma mun gurfanar dashi gaban ƙuliya , saboda yanzu abinda yake buƙata yanzu shine adalci. Kuma kotu ne mai iya bada wannan adalci“.

Tirƙashi, ashe dai haƙorin dariya shi yakan yi cizo. To Allah ya kyau ta, ya kiyaye mu aikin dana sani.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *