Kan Batun 19bn: Mun baku awanni Arba’in da takwas 48 daga Yanzu ku janye Kalamanku ko Kuma mu maka ku a kotu ~Gwamnatin kogi ga hukumar EFCC.

Rahotanni daga Jihar kogi A yau ranar Lahadi na cewa gwamnatin jihar Kogi ta musanta mallakar naira biliyan 19.3 da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC tace ta mayar wa babban bankin Najeriya CBN.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Juma’ar data gabata ne hukumar EFCC ta ce ta mayar wa CBN zunzurutun kudi har Naira biliyan 19.33 da ta kwato daga asusun bankin Sterling mallakin Gwamnatin kogi

Sai dai da yake magana da manema labarai a yau ranar Lahadi Mista Kingsley Fanwo, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, ya bayyana ikirarin a matsayin karya da kuma zunzurutun adawar Siyasa.”

Gwamnatin

Jihar ta kuma yi barazanar daukar matakin shari’a idan har EFCC ta kai sa’o’i 48 ba, ta janye wannan kalamai ba.

Fanwo ya bayyana cewa jihar Kogi ba ta da asusun ajiya da bankin Sterling, wanda bankin ya yi karin haske a cikin wasikar ta, mai kwanan wata 1 ga watan Satumba.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar ta bayar da lamunin ceto tun daga watan Oktoban 2019 kuma babu wani boyayyen kudi da Suka rage lamuni na jihar Kogi da za’a iya mayar da shi CBN ko kuma a daskarar da shi bisa umarnin kotu.

“Hukumar EFCC ta san haka, shi ya sa ta janye karar da ta shigar a Kotu kan asusun ceton inji shi.

“Gwamnatin Kogi kuma ba ta bude wani asusu na ceton albashin jihar Kogi, mai lamba Kamar haka 0073572696 ba, inda aka ce an ajiye kudaden an boye su kuma a yanzu an mayar da su ga babban bankin CBN,”

Fanwo ya kuma kalubalanci hukumar EFCC da ta bayar da cikakkun bayanai game da kayyade asusun ajiya, inda ya kara da cewa wannan na da nufin bata sunan siyasar Gwamna Yahaya Bello.

Muna jiran Sakon ku na neman afuwa cikin sa’o’i 48 daga yanzu yau, daga dukkan jami’an EFCC da kafafen sada zumunta na yanar gizo zuwa ga gwamna da daukacin gwamnati da Jama’ar jihar Kogi,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *