Karamin rikicin Jam’iya bai kawar da Hankalinmu wajen bunkasa jihar Kano ba.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce rikicin da ya barke a jam’iyyar APC a jihar ba zai kawar da hankalin gwamnatinsa na bunkasa jihar ba.

Ganduje, a cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar, ya fitar, ya bayyana haka a gidan gwamnati da ke Kano Lahadi a wajen taron masu ruwa da tsaki.

Ya ce: “Yana da matukar muhimmanci kowa ya san cewa hazakarmu ta siyasa da gogewar siyasarmu ba za su bari kananan rikicin jam’iyya su karkatar da hankalinmu wajen kara bunkasa jiharmu ta Kano ba.

“Abin

da ke faruwa wani bangare ne na al’adun dimokuradiyya.”
Ya ce taron an yi shi ne domin jaddada bukatar samar da zaman lafiya a jam’iyyar.

Bai kamata a ja da baya ba saboda rikicin jam’iyya na yau da kullun. Wannan abu ne na al’ada a tsarin dimokuradiyya, “in ji Ganduje.

Taron ya samu halartar Sanata Kabiru Gaya da ‘yan majalisar wakilai da kakakin majalisar dokokin jihar Kano da shugabannin kananan hukumomi da kuma shugabannin jam’iyyar APC na Unguwa da kananan hukumomi da na jahohi da dai sauransu.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *