Karo na karshe Ku fara kirga ragowar kwanakin da suka rage maku a duniya ~Shugaba Buhari ga ‘yan Bindiga.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa ‘yan bindiga cewa su kasance cikin shiri don murkushe su.

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a yau ranar Litinin yayin da yake mayar da martani kan kisan sama da mutane 30 a Goronyo, Jihar Sakkwato ranar Lahadi.

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya ce kwanakin ‘yan bindigar sun Kasance a takaice saboda karfin sojan da sojojin mu ke samu ta hanyar samun kayan aiki na zamani da tura su Zuwa ga ‘yan Bindigar.

Ya

yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya “kada su yanke kauna saboda wannan gwamnatin ta himmatu fiye da kowane lokaci don kare’ yan Najeriya daga kungiyoyin masu aikata kisan gilla wadanda ba sa girmama mutuncin rayuwar dan adam.”

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin Goronyo ya rutsa da su sannan ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hakuri yayin da sojoji ke yin dabarun yadda za su kai wa wadannan ‘yan bindiga hari.”
Ya ce: babban Agogon halakar ku yana tafe saboda ba za ku sake samun wurin buya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *